An bude katafaren dakin ajiya da wankan gawa a masallacin Izala a Gombe.
Daga Wakilinmu
Kungiyar Izala ta kasa reshen jihar Gombe, karkashin jagorancin shugaban ta na jaha Sheikh Salisu Muhammad Gombe, ta bude katafaren gidan wankan gawa a helkwatar kungiyar dake masallacin Bolari a cikin garin Gombe.
Sanata Sa'idu Alkali, sanata a zauren majalisar Dattawan Naijeriya mai wakiltar kananan Hukumomin Gombe, kwami, funakaye, Nafada da Dukku duka a jahar Gombe, ya samu halartar taron da kansa ba aike ba, kuma shi ya dauki dawainiyar aikin tun farko har zuwa yau karshe da ake taron budewa.
Sanatan yayi wannan aiki ne na sadaka mai gudana, Wanda ya zama irinsa na farko a jihohin arewa maso gabashin kasar Wanda yake mallakar kungiyar IZALA domin yaci gaba da samun lada har bayan rayuwar sa
Daga yau juma'a Juma'a 18th Rabi’ul Awwal 1444H.
14th October 2022, a hukumance an kaddamar da gidan ajiya tare da wankan gawa a masallacin JIBWIS dake unguwar Bolari a fadar Jihar Gombe.
Ayyukan da za'a fi maida hankali a kansu a wannan gida sun hada da Ajiyar gawa da bazai wuce kwana daya zuwa biyu ba. Za'a dinga gudanar da wankan gawa a wajen, sannan an tanadi babban na'urar sanyi na ajiyar gawa (Freezer) da sauran sinadarai da zasu hana gawa lalacewa kafin akai ga janaza. Kazalika baza a ajiye duk wani gawa da ya zama dameji ba, da sauransu, za'a karbi gawa a wannan gida ne kawai wadanda suka rasa rayuwarsu a mutunce.
Shugaban Izala na jihar Gombe Sheikh Salisu Muhammad Gombe ya yaba kwarai da irin wannan aiki da kai tsaye ya shafi al'umma, yace yin hakan farar dabara ce ga duk wani mai tunani, ya kuma kare da kira ga sauran 'yan siyasa da suyi koyi da irin wannan aiki da sanata alkali yayi wa kansa da addini, Wanda babu wani Abu zai zai biyo baya ga Wanda yayi irin wannan illa alkhairai daga Allah (SWT)
Mataimakin Shugaban Izala na tarayyar Naijeriya, kuma Hakimin Taliyawa, Sheikh Usman Isa Taliyawa na daya daga cikin manyan baki da suka halarci taron. Kazalika Shugabanni, malamai, Jami'an gwamnati, 'yan siyasa da sauran daidaikun jama'a ne suka samu halartan taron.