DAGA ABDULKARIM UMAR
Adai dai lokacin da dukkan alhazzan duniya ke dakon ranar ARAFAT ita ko hukumar hajji ta kasar saudiyya ta bullo da Wani sabon tsarin raba alhazzan gida biyu wasu su Isa muna kana daga bisani su wuce zuwa filin arfat wasuko Kai tsaye zasu wuce filin arfat.
Kasa alhazzan gida biyu da tayi nada nasaba da rage cinkoson alhazzai a birnin na Muna laakari da yawan alhazzan na bana .
Wannan nakunshene acikin wani jawabi Wanda Jami"in hulda da kama'a Nahukumar aikin hajj ta jahar Zamfara ,Mallam Bello Musa Sidi Sidi Magami yasanyawa hannu Kuma akarama manema labarai a birnin Gusau, hidikwatar jahar Zamfara.
To sai dai duk da wannan tsarin na raba alhazzan gida biyu mukam alhazzan mu na jihar zamfara nadaga cikin alhazzan da suka shiga sahun farko na samun Isa Birnin Muna tun Daren jiya wayewar garin yau litinin 26/6/23.
Wannan nasarar da alhazzan namu suka samu nada nasaba da kammala jigilarsu zuwa kasar saudiyya cikin lokaci Wanda Hakan yabasu damar kamma dukkan ibadar ziyara a birnin Madina suka Kuma koma birnin Makkah.
Yanzu haka dai kwamitin amirul hajj na jihar zamfara karkashin jagorancin Alhaji Musa mallaha talban gusau da sakataren sa Dr Aliyu Adamu Bormo da sauran da shugaban karamin kwamitin tent Hon kasimu sani kaura da mataimakin shi malam auwal khamis da sakataren kwamitin Alhaji yushau yahayya da Kuma shi kanshi sakataren hukumar hajji ta jahar zamfara Alhaji Anas shaaibu mafara da daraktoci na hukumar hajji dama sauran jamian hukumar da tawagar malammai suna tare da alhazzan jihar zamfara su dubu ukku da Dari daya da biyu a Birnin Muna domin tsara yadda zaayi sufurin alhazzan zuwa filin arfat.