DAGA ABDULKARIM UMAR
Kungiyar yanbanga takasa reshen jahar Zamfara Takai ziyarar Sada zumunci dakuma Neman shawara ga hedekwatar sojoji ta 1 BRIGADE Dake Gusau.
Kungiyar Dake karkashin jagorancin Kumandan Alh Rabi'u Bawa Maru. Takai wannan ziyarar ne Domin Neman Hadin Kan jami'an sojoji Wajen kawarda yanbindiga da Barayin Shanu dakuma kawarda miyagun laifukka afadin Jahar Zamfara bakidaya.
Alhaji Rabi'u Bawa Maru yakara dacewa sanin mahimmancin jami'an soji akasanan shiyasa kungiyar tazabi tafara kaiziyara awajensu Domin samun shawara da goyonbayan sojoji Wajen gudanarda ayukkan kungiyar..
Ajawabinsa Kumandan Hedekwatar sojoji tadaya Dake Gusau. Big General Sani Ahmad Ya yabawa shugaban kungiyar yanbanga takasa reshen jahar Zamfara dangane da wannan Ziyara dasuka kawomasa Kuma Yayi alkawalin baiwa kungiyar dukkanin goyonbayan dayadace Domin samun kawarda aikin badala acikin jahar Zamfara.
Haka Kuma yashawarci shuwa gabanin wannan kungiyar dasukasance masu bin doka da oda surika tuntubar jami'an tsaro Wajen aiwatarda ayukansu, sukuma kaucewa daukar doka da hannunsu.