Daga: Yahaya Mahi Na Malam Babba
Babban manajan gudanarwa na bankin Keystone reshen Gusau jihar Zamfara ya karɓi addinin musulunci, inda ya yi bankwana da tsohon addininsa na kiristanci bayan dogon nazari da ya gudanar.
Manajan bankin mai suna Femi Ajayi a baya, yanzu ya sauya sunansa zuwa Abdulrahim, tare da shan alwashin zai rungumi addinin da hannu biyu.
Babban limamin masallacin juma'a na Sheikh Abdullahi Gwandu da ke kan titin Byepass Sheikh Ahmad Ibn Umar Kanoma ne ya jagoranci manajan zuwa addinin na musulunci.
Wakilinmu, ya ruwaito cewa al'umma da dama sun yi farin ciki da shigar manajan bankin a addinin Musulunci, domin ya karɓi addinin ne a daidai lokacin da ake gudanar da huɗubar Juma'a.
Sheikh Ahmad Umar Kanoma, ya ja hankalin manajan da ya kyautata niyarsa ya kuma riƙa wannan addinin da hannu biyu, ta yadda zai sa waɗansu su yi koyi da shi musamman iyalansa.
No comments:
Post a Comment