Jami’an tsaro na ‘yan sanda a Zamfara sun yi nasarar kubutar da mutane tara (9) da suka hada da mata bakwai (7) da maza biyu (2) da aka yi garkuwa da su a ranar 11 ga Afrilu, 2023 a garin Kucheri da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Ceto wadanda abin ya shafa ya biyo bayan sahihan bayanai da aka samu daga wani 'dan kasa nagari wanda ‘yan sanda suka yi amfani da bayanansa, tare da samun nasarar ceto wadanda lamarin ya shafa.
Wadanda lamarin ya rutsa da su yayin da suke tare da ‘yan sanda, an duba lafiyarsu a asibitin ‘yan sanda dake Gusau, inda jami’an ‘yan sanda suka bayyana su sannan suka sake hadasu da iyalansu.