DAGA ABDULKARIM UMAR
Motocin sufurin alhazzan jihar zamfara jirgi na daya dazasu dawo gida yau laraba sun samu Isa filin jirgin sama na Mai alfarma Sarkin musulmi Abubakar na ukku dake sokoto.
Tawagar motocin na karkashin kulawar jamiin ICT na hukumar hajji Kuma mamba a kwamitin sufuri murtala Ismail gusau tare da Sanya idon ofishin jamiin hudda da jamaa na hukumar hajji Bello Musa sidi magami.
Acikin tawagar akwai jamiian tsaro na soja da DSS da civil defence da Yan sanda da Kuma road safety domin ba alhazzan kariya ga lafiyar su dama kayyayyakin su yayin rakiyarsu zuwa birnin Gusau.
Wannan nakunshene awata takarda da jami'in Hulda da kama'a Nahukumar aikin hajj ta jahar Zamfara Mallam Bello Musa Sidi Magami yasanyawa hannu Kuma akarabama manema labarai a birnin Gusau hidikwatar jahar Zamfara.
Hakama akwai jamiin hukumar hisba da Yan agaji da na kungiyar KTA dake taimakawa ga kula da kayan alhazzai da zaayi dakonsu zuwa gida .
A can bangaren sansanin alhazzan kuwa akwai tanadin jamiin tsaro da sauran kungiyoyin agaji da sauran jamiian hukumar hajji domin taimakama alhazzai idan sun shigo San sanin .