DAGA ABDULKARIM UMAR
KWAMITIN KULADA HEMOMIN AIKIN HAJJIN BANA NAJAHAR ZAMFARA KARKASHIN JAGORANCI ALHAJI KASIMU SANI NACIGA DARABA HEMOMIN GA ALHAZZAI AFILIN ARAFA.
DAYAKE YIMA JAMIIN HULDA DA JAMAA NA HUKUMAR HAJJI TA JIHAR ZAMFARA BELLO MUSA SIDI MAGAMI BAYANI AKAN YADDA AIKIN RABON HEMOMIN KE GUDANA SAKATAREN KWAMITIN MALAM AUWAL KHAMIS YACE KWAMITIN YAYI KYAKKAWAN TSARI NA TABBATAR DA RABA HEMOMIN GA DUKKAN ALHAZZANMU NA KANANAN HUKUMOMIN GOMA SHA HUDU DA KUMA BANGAREN SHUGABANNIN KWAMITIN AMIRUL HAJJ DANA SAURAN JAMIAN HUKUMAR HAJJI DA BANGAREN MALAMMAI DA YAN JARIDA DA KUMA SAURAN WAKILLAI .
MALAM AUWAL KHAMIS YA KARA DA CEWA KAMAR KOWACE SHEKARA ANFIDDA BANGAREN MATA DABAN NA MAZA ALHAZZAI DABAN KUMA TARE DA SANYA ALAMOMI A KWANE MASHIGI NA HEMAR ZAMFARA MAI DAUKE DA ALAMAR ATAMFA TA MATA ALHAZZAN JIHAR.
AUWAL KHAMIS YACE ANYI HAKANE DOMIN KAUCEWA GA BACEWAR ALHAZZAN JIHAR ZAMFARA LAAKARI DA CEWA DUKKAN HEMOMIN ALHAZZAN DUNIYA A MUNA DUKANSU KALA DAYANE .
YA KARA DA CEWA ABANGAREN WAAZI GA ALHAZZAN AKWAI TANADIN RARRABA MALAMMAI MASU WAAZI DAKUMA BADA SALLAH GA ALHAZZAN ABKOWACE HEMA TA HANYAR AMFANI DA AMSA AMO DA YAN JARIDA DAKE TARE DA ALHAZZAN KE AMFANI DASHI .
DAYAYI KARIN HASKE AKAN ABINCI AUWAL KHAMIS YA BAYYANA CEWAR AKWAI BANGAREN DA AKA WARE A CIKIN HEMAR DOMIN DAFANA ALHAZZAI ABINCI HAKAMA AKWAI TANADIN BANGAREN DA AKAYIMA JAMIAN LAFIYA A CIKIN HEMAR DON BADA AGAJIN GAGGAWA GA ALHAZZAN JIHAR ZAMFARA.
AUWAL KHAMIS YA KUMA KARA BAYYANA CEWA AKWAI WURAREN KEWAYAWA A CIKIN HEMOMIN GA ALHAZZAN MASU SON BUDE IDO AKWAI WANI BANGARE DA AKA KEBE NA JAMIAN HUKUMAR SAUDI MASU KULA DA HEMOMI WANDA WURINE NA HUTAWA DA AKAYIMA ADO DA TIKA TIKAN KUJERI NA ALFARMA DA TALABISHIN DA SAURAN NAURORIN SANYI DON SHAKATAWAR ALHAZZAI.
ABANGAREN NAURA MAI SANYYA JIKI AUWAL KHAMIS YACE A CIKIN KOWACE HEMA TA ALHAZZAI AKWAI AC DA KUMA WURAREN SANYA CAJIN WAYOYI DOMIN AMFANIN ALHAZZAN.
ITADAI MINA WANI SAN SANINE DA ANAN NE ALHAZZAN DUNIYA KE TARUWA KANA DAGA BISANI SU FITA ZUWA ARAFAT KUMA SU SAKE DAWOWA SU ZAUNA HAR TSAWON KWANKI UKKU DOMIN YIN JIFAR JAMRAT DA GABATAR DA SALLOLIN FARILLAH DA KUMA ADDUOI
No comments:
Post a Comment