Daga Muhammad Kwairi Waziri
Mai girma Gwamnan jihar gombe ya bayyana cewa, tun daga lokacin da kungiyar ASUU, ta fara yajin-aiki ake biyan malaman jami'ar jihar gombe albashin su, ba tare da sun yi aiki ba.
Muhammadu Inuwa Yahaya yace, zai dakatar da albashin malaman jami’arsa idan suka ki dawowa aiki.
Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya Kara da cewa duk tsawon watanni shida malaman jami’ar jihar Gombe ta GSU suke yajin-aiki, kuma ana biyansu kudi.
An gagara shawo kan ASUU a GSU A cewarsa, an yi kokarin tattaunawa da shugabannin jami’ar ta GSU da kuma reshen kungiyar ASUU na malaman jami’ar GSU, amma an gaza samun mafita.
Idan har malaman sun ki bude jami’ar domin a cigaba da karantar da yara kamar yadda aka bada umarni, gwamnatin jihar Gombe za ta daina biyan su albashi.
Gwamnan ya bayyana yadda yake biyan ma’aikatan jihar da ‘yan fansho albashinsu duk ranar 25 da 27 na kowane wata tun da ya zama gwamna.
No comments:
Post a Comment